This web page was created programmatically, to learn the article in its authentic location you possibly can go to the hyperlink bellow:
https://www.bbc.com/hausa/articles/cm2d7gjx0zgo
and if you wish to take away this text from our web site please contact us
Asalin hoton, NASA/JPL
-
- Marubuci, Rebecca Morelle
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science Editor
- X,
Wasu alamomin duwatsu da ba a saba gani ba da aka gano a duniyar Mars masu ƙunshe da wasu alamomin da ba a tabbatar ko mene ne ba na nuna cewa an taɓa rayuwa a duniyar a baya.
Wasu ɓaraguzan duwatsu da hukumar kula da sararin samaniyar Amurka, Nasa ta gano a gefen wani kogi mai cike da ƙura ne suka tabbatar da hakan.
An gano duwatsun masu wasu zane-zanen launin damisa da wasu dabbobi.
Masana kimiyya solar yi imanin cewa waɗannan alamomi solar ƙunshi ma’adinai da aka samar ta hanyar amfani da haɗe-haɗen sinadarai masu alaƙa da tsofaffin halittun Martian.
Mai yiwuwa ne waɗannan ma’adinan an samar da su ne ta hanyar halittar ubangiji, amma bincike na da muhimmanci domin cimma ƙa’idar hukumar Nasa kan abin da ta kira ”abubuwan da aka samar daga duwatsun”.

Hakan na nufin abubuwan da aka samu solar buɗe ƙofar bincike domin gano ko a an taɓa rayuwa a duniyar.
“Ba mu taɓa gudanar da irin wannan bincike ba a baya, don haka ina ganin wannan babban al’amari ne ,” a cewar Farfesa Sanjeev Gupta, masanin kimiyyar duniyoyi a Jami’ar London kuma ɗaya daga cikin masu binciken da aka wallafa a mujallar Yanayi ta ”Nature”.
“Mun samo wasu alamomi a jikin dutwatsun , waɗanda idan ka gan su, to akwai alamar cewa an taɓa rayuwa a wurin, don haka ba muna cewa mun gano an taɓa rayuwar a duniyar Mars ba, abin da muke cewa shi ne akwai alamun hakan”, in ji shi

Hanya ɗaya tilo da za a tabbatar da hakan shi ne ɗauko duwatsun zuwa duniyarmu domin gudanar da bincike.
Hukumar kula da sararin samaniyar Amurka, Nasa da ta Birtaniya Esa ta bayar da shawarar komawa duniya Mars domin fara rayuwa, sai dai yiwuwar hakan na cikin halin rashin tabbas.
Saboda rage kasafin kuɗin hukumar Nasa na 2026 da Shugaba Trump ya yi, lamarin da ya sa ƙudirin na Nasa ke fuskantar sokewa.
A yau, Duniyar Mars cike take da sanyi da ƙura. Amma biliyoyin shekarun da suka gabata akwai hujjojin da ke nuna cewa duniyar na da yanayi mai kyau da kuma ruwa, lamarin da ya sa ake ganin za ta kasance ɗaya daga cikin wuraren da za su yi kyau da rayuwa.
Kumbon Perseverance Rover, ya sauka a duniyar Mars a 2021, domin neman alamomin rayuwa a cikinta.
Kumbon ya kwashe shekara huɗu yana zaƙulo abubuwa a wani yanki na duniyar da ake kira kwazazzabon Jezero, wanda a baya ya taɓa kasancewa wani kogi mai gudana a cikin duniyar Mars.
Kumbon ya gano wasu duwatsu masu zane-zanen launin damisa a ƙarƙashin wani kogin da ya ƙafe a yankin da ake kira ”Bright Angel Formation”.
Ana tunanin duwatsun solar shekara biliyan 3.5, kuma nau’ikan dutwasun nan ne da ake kira hoge, masu kama da waɗanda ake samu daga taɓo.
“Mun fahimci cewa akwai wani abu mai kama da rayuwa da ya taɓa faruwa a wurin, don haka muna son faɗaɗa bincike”, a cewar Joel hurowitz ta jami’ar Stony Brook da ke New York, wadda ta kasance masu lura da kumbo.
Asalin hoton, NASA/JPL
Kumbon ya yi amfani da kayayaki da dama da ke cikin ɗakin gwaje-gwajensa wajen nazarin ma’adinan da aka samu a cikin duwatsun.
An kuma tattara bayanan tare da maido su duniyarmu domin faɗaɗa bincike.
“Muna tunanin cewa abin da muka gano shaida ce da ke nuna cewa an taɓa rayuwa a wurin mai cike da ƙurar da ke tattara a ƙarƙashin teku, saboda alamun cuɗanya da ka gani tsakanin ƙurar da kuma ƙwayoyin halitta, kuma waɗannan abubuwan biyu ne ke samar da sabbin ma’adinai,” in ji Dakta Hurowitz.
A wani makamancin yanayi a duniyarmu, cuɗanyar sinadarai ne ke samar da wasu ma’adinan da ake samarwa daga ƙwayoyin halitta.
“Wannan shi ne ɗaya daga cikin dalilan bayanan yadda waɗannan alamomi suka ƙara fito da abin da muke hasashe, kuma yake buƙatar zurfafa bincike,” in ji Dr Hurowitz.
Masana kimiyyar sun kuma auna yadda za a iya samar da ma’adinai ba tare da ƙwayoyin halita ba, inda kuma suka gano cewa hanyar halitta ta ubangiji ne kawai ke tsara hakan.
Haka kuma, za su buƙaci tsananin zafi, kuma dutwasun ba su yi kama da masu ɗaukar zafi ba.
Asalin hoton, NASA/JPL
Kumbon ya riƙa ɗauko samfurin abubuwa da dama daga duniyar Mars, ciki har da duwatsun da ya samo daga yankin ”Bright Angel Formation”na duniyar.
An taskance su a wani wuri domin sauko da su duniyarmu don gudanar da bincike a kansu kafin a mayar da su duniyar Mars.
To sai dai shirin hukumar Nasar na fuskantar tasgaro, yayin da Trump ya rage wa hukumar kuɗin kasafinta, to amma China na shirin ƙaddamar da nata binciken kan samfuran a 2028.
Yayin da ake ci gaba da tafka muhawara kan matakin, masana kimiyya sun zaƙu su fara aikinsu kan duwatsun.
”Muna fatan ganin waɗannan samfura a duniyarmu,” in ji Farfesa Gupta.
“Ina tunanin domin samun ƙwarin gwiwa, mafi yawan masana kimiyya za su yi fatan gani tare da binciken waɗannan duwatsu a duniyarmu – Wannan zai kasance ɗaya daga cikin gagarumin aikin da masana kimiyya za su yi.”
Asalin hoton, NASA/JPL
This web page was created programmatically, to learn the article in its authentic location you possibly can go to the hyperlink bellow:
https://www.bbc.com/hausa/articles/cm2d7gjx0zgo
and if you wish to take away this text from our web site please contact us
